A karshe dai mawaki Hamisu Breaker yayi magana akan zargin da ake masa na yaudarar matar aure

A karshe dai mawaki Hamisu Breaker yayi magana akan zargin da ake masa na yaudarar matar aure

Shahararren mawakin fina-finan Hausa, Hamisu Sa’idu Yusuf, wanda aka fi sani da Hamisu Breaker ya bayyana cewa batun da aka danganta shi da shi na cewa ya yaudari wata matar aure zuwa masana’antar fina-finan Hausa ya dauki lamarin a matsayin kazafi da kuma jarabta daga Allah, kuma yana fatan ALlah yasa ya ci wannan jarabawar.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata wani mawaki mai suna Aliliyo Mai Waka ya zargi Hamisu Breaker da laifin yaudaro wata matar takwaransa mawaki Adam Fasaha zuwa cikin harkar fim.

An yi zargin cewa tun kafin jarumar mai suna Momee Gombe ta fito daga gidan mijinta mawaki Hamisu Breaker yake hure mata kunne, wanda kuma bayan fitowar ta din ne aka soma ganin yana saka ta a cikin bidiyon wakokinsa, hakan yasa aka sake tabbatar da zargin da ake yi masa.

Sai dai a yayin da Breaker ya zanta da Rariya, ya bayyana cewa “Wallahi zargin da ake yi masu babu madogara bare tushe. Kazafi ne kawai, don kawai an ga na soma samun daukaka shine ake so a mata min suna.”

Breaker ya kara da cewa ko lokacin da aka saki Maryam din ya fi shekara bai yi ido hudu da ita ba.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.