Abubuwa guda 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari

Abubuwa guda 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari ya rasu a ranar Juma’a, amma an binne shi a safiyar ranar asabar. An binne shi a makabartar Gudu dake Abuja.

Sai dai akwai wasu al’amura masu matukar rikitarwa game da mutuwarsa, ga dai guda hudu daga cikin su:

  1. Hasashen Kemi Olunloyo: Tun baan da mai bawa shugaban kasa shawara ta musamman a fannin sadarwa ya tabbatar da mutuwar Abba Kyari, sunan Kemi Olunloyo ya cigaba da yawo a kafafen sada zumunta. Kemi diyar tsohon gwamnan jihar Oyo ce wacce a cikin kwanakin nan ta bayyana cewa wani babban jami’in gwamnatin Najeriya ya rasu sanadiyyar cutar Coronavirus. Duk kuwa da cewa ba ta sanar da ko waye ba, ta ce jami’in ya rasu ne tun kafin ranar Juma’a, a lokacin kuwa Abba Kyari ne ka dai yake jinya sakamakon cutar wanda ke da kusanci da fadar shugaban kasar.
  2. Shekarun haihuwar Kyari: Jim kadan bayan ya rasu, shafin yanar gizo na Wikipedia ya bayyana cewa yana cikin shekarunsa na 70 ne da doriya, amma kuma ba a bayyana ko shekaru nawa yake dasu takamaimai. Sai dai kuma kamar yadda Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta wallafa a shafinta ta bayyana cewa tashar talabijin ta TVC ta bayyana cewa an haifeshi ne a shekarar 1938 kuma ya rasu a shekarar 2020, inda hakan ke nufi yana da shekaru 81 a duniya.
  3. Asalin inda ya rasu: Ba kamar sauran mace-macen dake faruwa ba sakamakon cutar ta Coronavirus a Najeriya, har ya zuwa yanzu ba a bayyana inda Abba Kyari yayi jinya ba har ya rasu. Abu guda daya da aka sani shine kawai ya rasu a jihar Legas.
  4. Karya dokar nisantar juna yayin binne shi: Kamar yadda hotuna da bidiyo suka bayyana, manyan kasar nan da suka sallaci gawar marigayin basu nisanci juna ba. Haka zalika har zuwa wajen da aka binne shi a makabartar Gudu dake Abuja, manayn jami’an gwamnatin Najeriya sun kasance masu cudanya da juna.

Idan har za a tuna a ranar 3 ga watan Afrilun shekarar 2020, Lai Mohammed ya tabbatar da cewa koda gawar wanda ya mutu sakamakon annobar ce bai dace a kusance ta ba. Ya sanar da cewa tana dauke da kwayoyin cutar kuma ana iya dauka.

Yanzu haka dai hukumar kare hakkin dan adam tayi kira da ayi gaggawar killace manyan da suka halarci jana’izar tasa domin kar su kasance matsala a cikin al’umma, musamman idan aka duba irin sakacin da suka dinga yi, bayan rashin nisantar juna da suka yi.

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.