Aisha Tsamiya: Jarumar da aka yi ittifakin ba’a taba ganinta da shigar banza ba

Aisha Tsamiya: Jarumar da aka yi ittifakin ba’a taba ganinta da shigar banza ba

Kowa dai ya riga ya gama yiwa jaruman Kannywood musamman mata shaidar cewa abinda suke yi ya wuce kima, lura da yadda suke shege ayarsu a gari ta hanyar shiga ta badala da nuna tsiraici.

To amma kuma hakan bai zama cewa duka jaruman sun taru sun zama daya ba, domin kuwa a duk inda mutane suka taru suna wata mu’amala to dole za’a samu na Allah a ciki.

Wannan dalilin ne yasa Jaridar yanar gizo ta Facebook mai suna ‘Mikiya’ ta kalubalanci masu kallon fina-finan Hausa akan duk wanda ya kawo hoton fitacciyar jaruma Aisha Aliyu Tsamiya wanda tayi da kananan kaya ko kuma ta fitar da tsiraici zasu bawa mutumin naira dubu ashirin (N20,000)

Ga dai abinda jaridar ta ce: “Ko kuna son cinye gasar N20,000?”

“Kawo mana hoton jarumar fina finan Hausa Aisha Aliyu Tsamiya wanda ta saka kananan kaya wando ko riga masu bayyana surar jikin mace.

“Idan ka kawo kaci naira dubu ashirin (N20,000), jarumar ta samu shaida ta kuma kafa tarihi cewa ita ce mace daya tilo a cikin masna’antar da bata yin shigar banza.”

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

WhatsApp: +84329864278

This Post Has One Comment

  1. Eehh,karindai yakarakudiba,domin ba,aragemana ko,kwaboba da,dai matsin tattalin arzikine anan talaka zai Gane

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.