Allahu Akbar: Shekara 42 muna tare, Abba Kyari bai taba cin amana ta ba – Shugaba Buhari

Allahu Akbar: Shekara 42 muna tare, Abba Kyari bai taba cin amana ta ba – Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa tsohon shugaban ma’aikatanshi, marigayi Abba Kyari, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma’a, shekarar su 42 suna tare kuma bai taba cin amanarsa ba, koda yaushe yana nuna goyon bayansa a tare da shi.

A sanarwar da shugaban kasar yayi a ranar Asabar kan rasuwar Abba Kyari, ya ce sun hadu da Abba Kyari lokacin yana tsakanin shekaru 20 a duniya.

KU KARANTA: Abubuwa guda 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari

Ya ce: “Malam Abba Kyari, wanda ya mutu a ranar 17 ga watan Afrilun shekarar 2020, wanda yake da shekaru 67 sanadiyyar kamuwa da cutar Coronavirus, babban mai kishin Najeriya ne. Babban abokine a wajena kuma bai taba cin amana ta ba yanzu shekaru 42 kenan, bai taba nuna gajiyawa ba akan ayyukan da yake yi ga al’umma ba.

Shugaban kasar wanda ya yiwa iyalan shi ta’aziyya, ya bayyana shi a matsayin daya daga cikin mutane masu muhimmanci a Najeriya.

Buhari ya ce Abba Kyari na da matukar ilimi, wanda ya tabbatar da cewar komai ya tafi daidai a fadar shugaban kasa ba tare da an samu matsala ba.

Ya kara da cewa: “Malam Abba Kyari yafi kowa a cikin mu. Yana daya daga cikin mutanen da suka kokarta wajen kawo Najeriya matsayin da take a yanzu. Allah ya jikanka abokina.”

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.