An gano Santa yana Sallah a Masallaci ranar Kirsimeti

An gano Santa yana Sallah a Masallaci ranar Kirsimeti

Hotunan wani Santa wanda aka fi sani da ‘Baban Kirsimeti’ na ta yawo a shafukan sadarwa bayan an gano shi yana Sallah a Masallaci ranar Kirsimeti.

Wannan shekarar dai ta fita daban da sauran shekarun da aka yi bikin Kirsimeti a Najeriya.

Kwanakin baya an bayyana rahoton yadda wasu yara suka yiwa wani Santa dukan tsiya saboda ya hana su kyaututtuka.

Bayan wasu ‘yan kwanaki kuma, aka gano wani Santa din yasha barasa yayi tatul a wajen wani biki.

A wannan karon kuma sai gashi an hango shi wannan Santa din yana Sallah a Masallaci a ranar Kirsimeti.

Ranar da 25 ga watan Disambar nan ne dai aka gabatar da bikin Kirsimeti a jihohin Najeriya dama wasu sassa na kasashen duniya.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zumunta, domin samun labarai da dumi-duminsu.

Facebook: https://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitter: https://twitter.com/jaridarhausa

Email: info@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.