Babbar magana: Ana zargin Mawaki Hamisu Breaker da yaudaro matar aure zuwa harkar fim

Babbar magana: Ana zargin Mawaki Hamisu Breaker da yaudaro matar aure zuwa harkar fim

Wani labari da kafar watsa labarai ta rariya ta wallafa a daren jiya sun bayyana yadda wani mawaki ke zargin Hamisu Breaker da hurewa matar sa kunne ta kaso aurenta ta shigo harkar fim, rahoton dai yazo kamar haka:

Ana zargin shahararren matashin mawakin fina-finan Hausa, Hamisu Breaker Dorayi da laifin hurewa wata matar aure kunne har sai da ya yaudaro ta zuwa harkar fim din Hausa.

Ba wata bakuwa bace wacce ake zargin mawakin ya hurewa kunnen illa yarinyar da ake yawan gani yana daukar wakokin bidiyoyin sa da ita, wato Momee Gombe.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Momee Gombe ta taba auren daya daga cikin mawakan Hausa, wato Adam Fasaha wanda kuma na hannun daman Hamisu Breaker ne.

Aliliyo Mai Waka, daya daga cikin na hannun daman Adam Fasaha, ya bayyana cewa shekaru biyu da suka gabata, Adam Fasaha ya auri Momee Gombe, amma sai Hamisu Breaker ya dinga hure mata kunne ba tare da ya yi la’akari da cewa tana gidan miji ba, inda har ta kai ga asirin sa ya tonu har ya nemi gafarar abokin nasa kan cin amanarsa da yayi.

“Ina zargin Hamisu Breaker da hannu dumu-dumu a mutuwar auren abokina, kuma aminina wato Adam Fasaha,” cewar Aliliyo Mai Waka.

Aliliyo ya kara da cewa a yanzu irin wannan cin amanar ya zama ruwan dare a masana’antar fim din Hausa. Domin kuwa irin haka din ya faru tsakanin Adam A. Zango da tsohuwar matarsa Maryam A.B Yola, inda bayan ta fito daga gidan sa wasu ‘yan fim suka dinga yi mata wasu abubuwa domin a ci mutuncinsa. Haka kuma an yiwa mawaki Adamu Hassan Nagudu, yanzu kuma an dawo kan Adam Fasaha.

Aliliyo ya kara da cewa abin haushi da takaicin shine yadda bayan kwana biyu da sakin dayan da Adam Fasaha ya yiwa Momee Gombe, Hamisu Breaker ya tafi da ita jihar Bauchi yin aikin fim, inda suka dauki tsawon mako guda a can, inda ko idda ba a bari ta yi ba. Kuma a daidai lokacin Adamu yana kokarin ya mayar da ita gidansa tunda dama saki daya yayi mata. Inda aka kama wasu dake da hannu a wannan lamari.

Aliliyo bai tsaya a nan ba, ya kara da cewa ko shi Hamisu Breaker an so a kamo shi a lokacin, amma Adam Fasaha ya ce a bar shi saboda alakar dake tsakaninsu. Amma bayan kwanaki kalilan da aukuwar hakan sai Hamisu ya cigaba da jan yarinyar a jikinsa.

“Muna da kwararan shaidun da suka tabbatar mana da cewa ko a lokacin da take da aure, tana zuwa wurin Hamisu Breaker. Sannan kuma ba ta da wasu wakoki da take sauraro ko a gidan mijin nata da ya wuce wakokin Breaker.

A yayin da Rariya ta nemi jin ta bakin Breaker domin kare kansa kan wannan zargi da ake yi masa duk irin kiraye-kirayen da aka yi masa ta waya yaki dagawa, haka ma yaki amsa sakon kar ta kwana da aka tura masa. Ita ma kuma Momee Gombe an kira wayoyin ta a kashe.

Sai dai a wani bangaren Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta samu damar tattaunawa da daya daga cikin makusantan Hamisu Breaker a masana’antar Kannywood wato Jarumi Ayatullahi Tage, inda ya karyata wannan batu sannan ya ce farfaganda ce ta neman suna kawai.

Sai dai kafar watsa labarai ta Kannywood Exclusive sun yi dacen samun magana da Momee Gombe, inda ita ma ta karyata wannan batu ta kuma ce, ta yaya za ace wani ya zuga ta ta kashe aurenta bayan ita ba yarinya bace, hasalima babu wani dalili haka kawai Adam Fasaha ya rubuta mata saki tana amarya ko wata biyu ba tayi da auren sa ba.

To Allah dai ya kyauta.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.