Bidiyon Tsiraici: Ana shirin korar Maryam Booth da Safara’u ‘Kwana Casa’in’ daga Kannywood

Bidiyon Tsiraici: Ana shirin korar Maryam Booth da Safara’u ‘Kwana Casa’in’ daga Kannywood

Wata majiya ta bayyana shirye-shiryen da ake na korar jaruman Kannywood biyu mata da bidiyon tsiraicin su ya fita a farkon watan Fabrairun da ya gabata, wato jaruma Maryam Booth da Safiya wacce aka fi sani da Safara’u ta cikin shirin ‘Kwana Casa’in.

Wannan sanarwa ta fito ne daga kafar yada labarai ta Kannywood Exclusive da suka wallafa a shafukan su na sada zumunta, inda suka ce:

“Akwai yiwuwar nan da wani dan lokaci, za a ga sanarwar dakatar da Maryam Booth da kuma Safiya, wadda aka fi sani da Safara’u Kwna Casa’in daga fitowa daga fina-finan Hausa kwata-kwata.

“Sai dai ana zargin ladabtarwar ba ta rasa nasaba da wani bidiyon tsiraicin su da ya fita a farkon watan Fabrairun da ya gabata.”

Idan baku manta ba dai a farkon watan Fabrairun nan da ya gabata, bidiyoyin suka fita, inda na jaruma Maryam Booth wani ne ya dauke ta har anga lokacin da take kokarin dakatar da shi ta hanyar kwace wayar daga hannunsa, inda har ta kai ga maganar yanzu haka ta isa gaban alkali ana shari’a tsakanin ta da wanda ake zargin ya nada tare da sakin bidiyon bayan yayi mata barazana ya karbi kudade masu yawa a hannunta.

Bayan wasu ‘yan kwanaki kuma sai ga bidiyon jaruma Safara’u shi ma ya bayyana, wanda shi nata yafi muni, inda ta dauki waya ta nuna kowane sashe na tsiraicinta kuma kawo yanzu ba ta fito ta karyata ko ta nuna nadamar abin da tayi ba.

A bangaren Maryam Booth jim kadan bayan fitar bidiyon nata mahukunta a masana’antar sun bayyana sanarwar cewa baza su kore ta ba, domin zaluntar ta aka yi kuma bata yi abin da sunan fim ko da son ranta ba, inda suka tabbatar da matsayar su kan cewa baza su kore ta ba.

Amma ga dukkan alamu baya ta haihu domin bullar wannan bidiyo na Safara’u ya tayar wa da Maryam Booth balli, inda wala’alla hakan ne yasa ake shirin yi musu kudin goro don magance faruwar lamarin a gaba.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.