Da Duminsa: Kungiyar Al-Qaeda ta dauki alhakin harin da aka kaiwa Sarkin Potiskum

Da Duminsa: Kungiyar Al-Qaeda ta dauki alhakin harin da aka kaiwa Sarkin Potiskum

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-Qaeda, ta bayyana dawowar ta Najeriya bayan ta dauki alhakin harin farko da ta kai a nahiyar Afirka tun shekarar 2013.

Idan ba a manta ba a ranar Talatar da ta gabata, an kashe kimanin sojojin Najeriya guda shida bayan wasu ‘yan ta’adda da suka yi shigar sojoji sun yi musu kwanton bauna akan babban titin Kaduna zuwa Zaria.

Wadannan sojoji suna daga cikin tawagar Sarkin Potiskum na jihar Yobe, wanda aka bayyana cewa shine wanda suka nemi kashewa.

Duk da dai hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa sojoji shida ne kawai aka kashe a harin, amma wasu majiyoyin sun bayyana cewa sojojin da aka kashe sun kai kimanin 30, sannan kuma an sanar da cewa wasu sojojin an neme su an rasa.

Kamar yadda jaridar 1st News ta ruwaito, kwatsam sai ji aka yi, kungiyar ta Al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin, inda ta bayyana kashe sojoji da yawa da kuma bata kone motoci masu yawa, haka kuma kungiyar ta bayyana sace sojoji da kuma mutanen gari, sai dai kungiyar ba ta bayyana cewa Sarkin Potiskum din suka kaiwa harin ba.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebook: https://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitter: https://twitter.com/jaridarhausa

Email: info@jaridarhausa.com

WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LjKaWUQXVpNI5p8mEZphN1

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.