Ganduje ya kori kwamishinan ayyuka na jihar Kano da ya nuna farin cikinshi a fili da mutuwar Abba Kyari

Ganduje ya kori kwamishinan ayyuka na jihar Kano da ya nuna farin cikinshi a fili da mutuwar Abba Kyari

Mai girma gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kori kwamishinan ayyuka, Injiniya Mu’azu Magaji daga kan mukaminsa biyo bayan kalaman murnar mutuwar shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Marigayi Abba Kyari da yayi a shafinsa na Facebook.

A sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamna Ganduje ya bayyana cewa abin da kwamishinan ya aikata na murna da mutwar Abba Kyari ba abu ne mai kyau ba, ya saba ka’ida, kuma abu ne wanda gwamnatinsa ba za ta zuba ido ta kyale mutum mai mukami a cikinta yana aikata su saboda wata manufa tasa ta kashin kanshi ba.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana cewa wannan hukunci ya fara aiki yanke take ba tare da bata lokaci ba na korar Mu’azu magajin daga kujerar sa ta kwamishinan ayyuka da kayan more rayuwa a jihar Kano.

KU KARANTA: Mutum 12 da sun kamu da cutar Coronavirus a jihar Kano, yayin da yawan masu ita ya kai 407 a Najeriya

Kyari ya rasu a ranar Juma’a bayan kamuwa da cutar Coronavirus, inda aka binne shi a makabartar Gudu dake Abuja a jiya Asabar, kamar dai yadda addinin Musulunci ya tanada.

A jiya ne dai kwamishinan ayyukan na jihar Kano ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook inda yake nuna farin ciki da mutuwar Abba Kyari, inda yake bayyana hakan da samun cigaba ga Najeriya.

Kwamishinan wanda ya hada rubutu cikin harshen Turanci da Hausa ya ce: “Win win… Nigeria is free and Abba Kyari ya mutu a cikin annoba… Mutuwar shahada in har da imani ya mutum ya cika.”

Haka kuma kwamishinan ya kara wani rubutu, inda ya ce dama ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar yayi girma da yawa saboda haka a raba shi gida biyu.

This Post Has One Comment

  1. best cbd oil

    I all the timeKu ajiye sunana da adireshin email dina a shafinku idan na aiko da sharhied this blog post page to all my contacts, as if like to read it next my friends will too.|

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.