Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Allah ya yiwa mahaifin Umar M Shareef rasuwa

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Allah ya yiwa mahaifin Umar M Shareef rasuwa

A jiya da daddare ne muke samun labarin rasuwar mahaifi ga jaruman Kannywood Umar M Shareef, Abdul M Shareef da kuma Mustapha M Shareef.

Mun samu sanarwar ne daga daya daga cikin ‘ya’yan, inda ya wallafa a shafinsa cewa:

“Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, ina mai alfahari da samun mahaifi kamar ka, domin kuwa kayi mana dukkan abinda ya kamata mahaifi ya yiwa ‘ya’yansa, Allah ya jikanka da rahama Allah ya gafarta maka, Allah ya sanya Aljanna ta zama mazauninka, Allah ya yafe maka dukkan kura-kuranka.

“Ya Ubangiji muna godiya a gareka..”

Take ‘yan uwa da abokanan sana’a suka cika shafukan sada zumunta da addu’o’i na neman gafara ga wannan uba ga ‘yan fim din wanda ya amsa kiran mahalicci tare da nuna alhini da jajantawa ‘ya’yan nasa da makusantan su.

Za ayi jana’izarsa a yau a gidansa dake Rigasa ‘yan kifi a cikin garin Kaduna muna fata Allah yayi masa Rahama ya kuma basu hakurin jure rashin sa.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.