Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 47 a jihar Katsina duk da annobar Coronavirus da ake fama da ita

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 47 a jihar Katsina duk da annobar Coronavirus da ake fama da ita

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane 47 da ‘yan bindiga suka yi a jihar Katsina a wasu hare-hare da suka kai a kauyukan jihar.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana haka, ya ce: “A ranar 18/04/2020 da misalin karfe 12:30 na dare, ‘yan bindiga masu yawan gaske dauke da bindigogi masu kirar AK-47 sun kai hari kauyen Kurechi dake karamar hukumar Danmusa cikin jihar Katsina.”

Ya cigaba da cewa: “Mutanen kauyen suma sunyi kukan kura kan ‘yan bindigar suka kore su. Daga baya, ‘yan kauyen sun fara kone rumbunansu da babu komai a ciki domin tabbatar da tsaron dabbobinsu da kuma hana ‘yan bindigar dawowa.

“Sai dai kuma, lamarin ya canja a lokacin da wasu ‘Yansakai suka fara kone rigar wasu fulani a Aibon Mangwaro dake cikin karamar hukumar ta Danmusa.

KU KARANTA: Tashin hankali: Kansila ya arce da buhunhunan shinkafa 30 da za a bawa talakawan yankinshi tallafi

“Duka dai a ranar, da misalin karfe 3:00, akwai rahoton hare-hare da akai kai kauyuka daban-daban a karamar hukumar Danmusa, Dutsinma, da Safana.

“A kauyen Kurechin Atai dake Danmusa, an kashe mutane 14. A Kurechin Giye da Kurechin Dutse duka dake karamar hukumar Dutsinma, ‘yan bindigar sun kashe mutane 10. Haka kuma a kauyen Makauwachi da Daule, ‘yan ta’addar sun kashe mutane 23,” ya ce.

“Tuni jami’an hukumar hadin guiwa na ‘yan sanda, sojoji, sojin sama, jami’an Civil Defence da DSS, sun bazama yankin suna dauki ba dadi da ‘yan bindigar,” ya bayyana.

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.