Jerin abinci 7 da suke cirewa mutum matsananciyar damuwa – Likita

Jerin abinci 7 da suke cirewa mutum matsananciyar damuwa – Likita

Kwararrun likitoci masu duba ma’abota tabin hankali sun yi kira ga jama’a da su guji yawan saka kansu a matsananciyar damuwa. Hakan na daga cikin abububwa da ke haddasa tabuwar hankali.

Mutum kan fada cikin matsananciyar damuwa ne idan bashi da halin samun biyan wata bukata ko kuma samun wani abu da aka sa a gaba.

Sai dai kuma, abinda ba a sani ba shine yawan shiga damuwa baya sa biyan bukata sai dai a fada cikin hadari da yakan kai ga tabuwar hankali a lokuta da yawa.

Marissa Laliberte likita ce a kasar Amurka kuma ta bayyana cewa akwai wasu abinci da ke dauke da sinadaran da suke taimakawa wajen hana damuwa. Abincin sun hada da:

1. Ayaba

Ayaba na dauke da sinadarin ‘Vitamin B6’ wanda ke assasa samuwar sinadarin Neurotransmitter Serotonin wanda ke ingantawa tare da sa fara’a a zuciyar mutum. Karancin wannan sinadarin kuwa na sa mutum ya fada damuwa.

2. Ruwa

Shan ruwa na daga ciikin hanyoyin da suke kawo yayewar matsananciyar damuwa. Bai kuma kamata a ji kishi ba kafin a nemi ruwa ba. Karancin ruwa a jikin mutum na cutar da kiwon lafiya.

3. Beat

Beat wani abinci ne mai kama da dankalin hausa sai dai shi ja ne a ciki da waje. Ana iya cin shi danye ko dafaffe amma masana sun ce ana samun sinadarin inganta lafiyar ne idan an ci danyen.

4. Kifi

Kifi na dauke da sinadarin Omega 3 wanda ke kaifafa kwakwalwar mutum. A dalilin hakan, likitan tayi kira ga jama’a da a lazimci cin kifii domin lafiyar kwakwalwa.

5. Bakar alawar cakulet

Likitocin sun tabbatar da cewa shan cocoa rigakafi ne wajen gujewa kamuwa da cutukan hawan jini, ciwon siga, karfaffa karfin ido da sauransu.

6. Alkama

Bincike ya nuna cewa alkama na daga cikin abincin da ke sanya farin ciki domin likitoci kan shawarci matan da suka dena haihuwa da su rika cin alkama don gujewa matsananciyar damuwa.

7. ‘Ya’yan itatuwa

‘Ya’yan itatuwa kamar su tuffa, lemu, fiya, gwaiba da sauransu na sanya farin ciki sannan kuma shayi mai madara na taimakawa ba kadan ba.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.