Kasuwa tayi wuya: Karuwai sun rage farashin kwanciya da su don su samu kwastomomi a jihar Legas, duk da fargabar Coronavirus da ake a jihar

Kasuwa tayi wuya: Karuwai sun rage farashin kwanciya da su don su samu kwastomomi a jihar Legas, duk da fargabar Coronavirus da ake a jihar

Titi Ipodo, dake Ikeja a jihar Legas, yana daya daga cikin titunan da har yanzu ake cigaba da dan harkoki a ciki a jihar Legas tun bayan sanya dokar hana zirga-zirga a jihar kimanin makonni uku da suka gabata.

Kwatsam yana tafiya sai ji yayi anyi masa magana, daya daga cikin wakilan jaridar Punch kenan wanda ya kai ziyara yankin.

“Hi, Hello” wasu ‘yan mata guda uku kenan da suke kai kawo a gaban wani otel dake kan titin.

“Zo muje dakina,” cewar daya daga cikin ‘yammatan da bata wuce shekaru 20 ba a duniya, yayin da taja wakilin jaridar Punch din zuwa daya daga cikin dakunan otel din.

“Sun ce Coronavirus na ko ina a kasar nan, amma ni na tabbata baza ta kama ni ba da ikon Allah,” ta kara da cewa yayin da take kokarin jan hankalin wakilin Punch din yayi lalata da shi, inda shi kuma yaki amincewa.

KU KARANTA: To fa: Dalibi dan Najeriya ya yiwa karuwa fyade a kasar Hungary

“Babu wata cutar Coronavirus a Najeriya,” cewar budurwar mai suna Blessing, yayin da ta bukaci ya zauna akan gadon dakinta. “Mutum nawa ka gani suna dauke da ita a Najeriya?” ta musanta maganar duk kuwa da cutar ta kama daruruwan mutane ta kuma kashe masu yawa a Najeriya.

Blessing ta yadda cewa Coronavirus karya ce kuma ana amfani da ita ne wajen cinye kudin kasa. “Naji an ce ta shiga jihohi da yawa, karya ne gwamnati ce kawai take so ta kashe kudin al’umma. Za su saci kudin har su gaji.”

“Idan har cutar na nan, mu kullum muna nan, mene yasa mu bata kama mu ba. Babu wannan cutar a ko ina a Najeriya,” ta ce.

Bayan sun dauki lokaci suna ciniki, a karshe Blessing ta amince akan za ta karbi naira dubu daya (N1,000) daga wajen wakilin Punch.

Sai dai kuma abin bai yiwa Blessing dadi ba, bayan wakilin Punch din ya tashi ya fita daga dakin, inda ta bayyana mishi cewa yau bata samu kwastoma ko daya ba.

“Inda na san haka ne bazan tsaya na bata lokacina ba wajen magana da kai. Yanzu mai gidan nan za tayi tunanin na kwanta da kai ne,” ta ce.

Haka a Toyin Street, wata karuwa ita ma da ta saba karbar naira dubu takwas idan za a kwanta da ita, ta rage farashi zuwa naira dubu uku na kwana daya baki daya.

Ita ma wannan karuwa ta bayyana rage farashin saboda matsalar da annobar Coronavirus ta kawo Najeriya.

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.