Labari mai dadi: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 105

Labari mai dadi: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 105

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa rundunar sojin ‘Operation Lafiya Dole’ ta kashe ‘yan kungiyar Boko Haram 105 a wani bata kashi da suka yi da su ‘yan kwanakin nan.

A wata sanarwa da hukumar sojin ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, Col. Sagir Musa a ranar Lahadi 19 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa an kashe ‘yan ta’addar a yankin arewa maso gabashin jihar Yobe a kusa da kauyen Buni Gari, bayan Brigadier General Lawrence Araba ya bi diddigin inda suke.

Sojoji guda biyu sunji raunika sanadiyyar wannan hari, sannan an kwace makamai masu yawan gaske daga wajen ‘yan ta’addar.

KU KARANTA: Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 47 a jihar Katsina duk da annobar Coronavirus da ake fama da ita

Shugaban hukumar sojin Yusuf Buratai ya nuna farin ciki matuka bayan an kai masa rahoton wannan nasara da sojojin suka samu a lokacin da ya kai musu ziyara a sansanin su.

“Shugaban hukumar sojin Najeriya, Lt Gen. Tukur Yusuf Buratai, ya yabawa sojojin Najeriya akan namijin kokarin da suka yi na kashe ‘yan ta’adda 105 a kauyen Buni Gari dake karamar hukumar Gujba cikin jihar Yobe a ranar Asabar 18 ga watan Afrilun shekarar 2020.

“Buratai ya kaiwa sojoji biyu da suka ji raunika a lokacin artabu da ‘yan ta’addar, haka kuma ya kai wa wasu sojojin dake asibitin Damaturu ziyara wadanda aka kwantar tun kafin a fita wannan artabu.

“Araba ya bayyanawa Buratai cewa sun samu nasarar wannan hari ne bayan samun labarin harin da ‘yan ta’addar suke shirin kaiwa kauyen.

Makaman da aka samu a hannun ‘yan ta’addar sun hada da bindigogi masu kirar AK-47 guda 5, da GPMG guda 3, Duska Anti Aircraft guda 1, da dai sauran su, bayan makaman an samu kwayoyi masu yawan gaske.

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.