Masu arzikin duniya sun sha alwashin tallafawa takalawa da abinci a wannan lokaci

Masu arzikin duniya sun sha alwashin tallafawa takalawa da abinci a wannan lokaci

Kasashen G20, wadanda suka fi ko ina karfin tattalin arziki a duniya, sun sha alwashin samarwa da talakawan duniya isashen abinci a wannan lokaci da ake fama da annobar Coronavirus.

Hakan dai ya biyo bayan gargadin da Majalisar Dinkin Duniya tayi na cewa, masu fama da matsalar yunwa a duniya zasu karu a wannan shekarar.

Wannan dai na zuwa ne bayan hukumar dake da alhakin samar da abinci a Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa akwai yiwuwar wadanda ke cikin matsalar yunwa a duniya ya karu zuwa miliyan 265 a wannan shekarar sanadiyyar cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Allahu Akbar: Ashe Abba Kyari ya dauki nauyin marayu 150 na tsawon shekara 10 kafin Allah ya karbi rayuwarshi

Ministocin noma na kasahen na G20, sun sanar da cewa zasu hada kai suyi aiki tare don ganin cewa an samu yawaitar kayan abinci a duniya, ta hanyar rabasu ga kasashen duniya domin talakawa su amfana.

Ministocin sun sanar da hakane a wani taro da kasar Saudi Arabia ta jagoranta a birnin Riyadh, sun ce suna aiki tukuru domin ganin kayan abinci basu tashi ba a kasuwannin duniya.

A kididdigar da aka fitar a shekarar da ta gabata, ta nuna cewa mutum miliyan dari da talatin da biyar (135m) ne suke fama da matsalar yunwa a duniya, inda a wannan karon hasashe ya nuna cewa adadinsu na iya karuwa ya kai kimanin mutum miliyan 265, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, sanadiyyar barkewar annobar Coronavirus a kasashen duniya.

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.