Matawalle zai ceto rayuwar Ibrahim wanda aka yankewa hukuncin kisa a kasar Saudiyya

Matawalle zai ceto rayuwar Ibrahim wanda aka yankewa hukuncin kisa a kasar Saudiyya

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya ce yana kokari na karshe wajen ceto rayuwar Ibrahim wanda yake dan asalin jihar Zamfara, da aka yankewa hukuncin kisa a kasar Saudiyya.

Gwamnan ya bayyana hakane bayan alwashin da ya dauka na ceto rayuwar duk wani mutumin jihar Zamfara dake cikin wani hali.

Wannan sanarwa ta fito daga wata takarda da mai taimakawa gwamnan na musamman a fannin yada labarai, Mr. Zailani Bappa, ya sanya hannu kuma ya sanar da hakan ga manema labarai.

Zailani ya bayyana cewa gwamnan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis dinnan da ta gabata domin ya roke shi akan ceto rayuwar Ibrahim wanda aka sanya ranar yanke masa hukunci a wannan makon mai zuwa, saboda zargin kama shi da miyagun kwayoyi.

Ibrahim da yake masani a fannin addinin Musulunci, anyi kuskuren kama shi da kwayoyi, inda har aka kai shi kotu, rashin lauya da zai tsaya masa yasa ake tsare dashi. Da farko dai wasu kananan kotu guda a Jedda sun kori karar tashi saboda rashin cikakkiyar shaida daga wajen masu kai karar.

Kamar yadda Jaridar Prime Time News ta bayyana, a halin da ake ciki yanzu dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari’a, Abubakar Malami da ya sanya baki a maganar Ibrahim din.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebook: https://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitter: https://twitter.com/jaridarhausa

Email: info@jaridarhausa.com

WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LjKaWUQXVpNI5p8mEZphN1

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.