Sabon bincike: Jemage ne ya kawo cutar Coronavirus duniya – WHO

Sabon bincike: Jemage ne ya kawo cutar Coronavirus duniya – WHO

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar da cewa binciken da ta gabatar ta samo wasu hujjoji dake nuna cewa cutar Coronavirus da ta addabi kasashen duniya ta samo asali ne daga jemage, a kasar China a karshen shekarar da ta gabata.

Hukumar ta sanar da cewa babu wani wanda ya kirkiri cutar a duniya, kamar dai yadda wasu mutane suke zargi.

A satin da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa na gabatar da binciken kwa-kwaf domin gano cewa ko wani ne ya kirkiri wannan cuta ta Coronavirus a birnin na Wuhan dake kasar China.

KU KARANTA: Masu gidajen haya a kasar Kenya sun yafewa duka mutanen dake haya kudin haya daga nan har zuwa lokacin da annobar Coronavirus za ta wuce

Mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya, Fadela Chaib ta tabbatarwa da manema labarai a birnin Geneva, inda ta ce hujjojin da suka samu sun bayyana cewa wannan cuta ta samo asali ne daga jemage.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta kama sama da mutane miliyan biyu da rabi, inda kuma ta kashe kimanin mutum dubu dari da tamanin, amma an samu kimanin mutum dubu dari bakwai da doriya da suka warke daga cutar.

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.