Sai Buhari ya kori shugabannin tsaron Najeriya sannan za a samu zaman lafiya – Kadariya Ahmed

Sai Buhari ya kori shugabannin tsaron Najeriya sannan za a samu zaman lafiya – Kadariya Ahmed

Shahararriyar ‘yar jaridar nan Kadariya Ahmed ta sanar da cewa, babban abinda ke damun Najeriya shine matsalar tsaro, kuma ba za a samu tsaro ba har sai shugaba Buhari ya kori manyan shugabannin tsaron kasar nan, saboda sun kasa tabuka komai.

Kadariya ta bayyana hakane a hirar da tayi da Aminiya a jiya Asabar da Yamma, a lokacin da ta halarci taron da aka shirya a jihar Legas domin bitar halin da kafafen yada labarai ke ciki da kuma yadda ake cin zarafin ‘yan jarida da sauran mutanen kasa.

A bayaninta ta ce yanzu kungiyar Boko Haram suna kara karfi a yankin Borno da Adamawa, “Kaga yanzu ‘yan ta’addar Boko Haram kara karfi suke, a jihohin Borno, Yobe da Adamawa kullum sai nayi rigima, mahaifata Zamfara a baya an dan fara samun rangwamen lamarin, amma yanzu barayin mutane sun sake tasowa da karfin su, haka yankin Kudancin kasar nan suma suna fama da tasu matsalar, saboda haka tsaro shine babbar matsalar Najeriya a yau,” inji ta.

Haka kuma a bangaren jarida, Kadariya ta bayyana cewa ‘yan jarida da kafafen yada labarai na kasar nan suna taka muhimmiyar rawa wajen tada zaune tsaye, yayin da idan wani abu ya faru maimakon su nemo inda matsalar take, sai dai su buge da bayyana dan kabila kaza, ko kuma dan addini kaza ne yayi abu, “Sai kaji ana Fulani ne ko Bayarabe, ko kuma Musulmi ne ko Kirista, duka wannan hanyoyi ne na raba kan jama’a, saboda haka mutane su hada kansu su nemi ‘yanci wajen mahukunta ko kuma a hada baki a fuskanci gwamnati da murya daya,” cewar ta.

A karshe Kadariya ta bayyana cewa a tsari irin na dimokuradiyya, kamata yayi a bawa mutane damar fitowa su bayyana ra’ayinsu, idan anyi musu wani abu da bai kamata ba.

Haka kuma ta bukaci gwamnati ta dinga tsayawa tana sauraron koken al’umma, ba sai sun kai ga fitowa sunyi zanga-zanga ba.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

WhatsApp: +84329864278

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.