Soyayya ta zama kiyayya tsakanin Darakta Aminu S Bono da jaruma Maryam KK

Soyayya ta zama kiyayya tsakanin Darakta Aminu S Bono da jaruma Maryam KK

Hausawa su kan ce so hana ganin laifi ko kuma ace wanda ya soka ya gama yi maka rana, amma sai dai wannan wata soyayya ce ake yi a masana’antar Kannywood, wacce bayan tayi kaurin suna aka buge da nunawa juna yatsa tsakanin fitaccen Darakta Aminu S Bono da jaruma Maryam KK.

Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa, da farko dai anji kananan maganganu na tashi tsakanin masoyan guda biyu, inda har ita Maryam ta wallafa rubutu a shafinta mai nuni da tabbacin sabanin dake tsakanin ta da uban gidan nata kuma saurayinta, hakan ya sanya wani dan jarida Aliyu Dalhatu ya tuntube su don jin yadda lamarin yake.

Koda ya tuntubi Darakta Aminu S Bono anji shi yana alakanta abin da Maryam tayi masa da hange da kuma cewa dama can soyayyar tayi tane da wata manufa ta cimma buri, yanzu kuma da take ganin wuyanta yayi kauri ta isa yanka, sai take hangen wanda yafi shi abin hannu, inda shi kuma ya bayyana cewa yana ganin ya dauketa kamar kanwa ce ko ‘ya.

Da aka tambayeshi kan zargin da ake masa na cewa ya ce tunda ta rabu dashi tata ta kare a masana’antar, daraktan ya musanta hakan, inda ya ce inda shi ma zai kamata da laifi akan maganganun da ta fada akan sa cikin fushi da abun yafi haka muni, musamman ma a kwanakin baya da suka samu wani sabani wanda ya ce ba zai bayyana abin da tayi ga duniya ba, saboda abu ne na gyaran tarbiyya.

Koda dan jarida Aliyu Dalhatu ya tuntubi Maryam sun tattauna, ita ma yaji ta bakinta, amma daga baya ta kira ta rokeshi akan kada ya wallafa abin da tace a tattaunawar ta su domin wasu da take jin nauyinsu sun kira ta sun ce ta bar maganar, saboda haka idan maganganun ta suka fita za su ga tamkar ta raina su.

Maryam KK dai jaruma ce mai tasowa da ta taka rawa a wakoki da dama wanda kuma mafi akasari Aminu S Bono din ne ya bada umarni, ita ce kuma jarumar da kwanakin baya iftila’i ya afka mata ta shiga hannun masu garkuwa da mutane a karshe Allah ya kubutar da ita.

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.