Takaitaccen tarihin kofofin Kano guda 13

Takaitaccen tarihin kofofin Kano guda 13

Kofofin Kano guda goma sha uku, kofofi ne da suka samo asali fiye da shekaru dubu da suka wuce, tun zamanin Bagauda wanda ya fara gina kofofin Kano, wato zamanin Sarki Warisi, wanda shine ya fara gina Badala.

Kofofin dai sun faro ne tun a shekara ta dubu daya da dari uku (1300), inda ake da kofofi guda shida a wannan lokaci, sai a karni na goma sha biyar, lokacin Sarki Muhammadu Rumfa aka kara kofofi guda hudu, sannan zamanin Sarki na Zaki aka kara kofofi guda uku.

Tarihi ya nuna cewa bayan zuwan Turawa sai aka kara kofofi guda biyu, wato Kofar Famfo da Sabuwar Kofa.

Wani masanin tarihin masarauta dake jami’ar Bayero ta Kano, Dr. Tijjani Muhammad Naniya ya bayyana dalilin kafa kofofin Kano.

“An kafa sune a yanayi na kasa wacce take shimfidaddiya, sadarwa tana da sauki, kuma an kafa su a yanki mai arzikin ruwa, mai arzikin noma, mai arzikin ma’adanai, to dole mutane za su so su zo wajen domin su ci albarkar wajen. Hakan sai ya kawo za’a iya kawo farmaki na yaki.

“Waje da yake a shimfide baka da tsaro to dole sai ka nemawa kanka tsaro, tsaron da zaka yi shine ka yiwa kanka katanga, ka kare kanka, to wannan shine asalin yin Badala.

“To kuma idan kayi Badala ka rufe ko’ina babu hanyar wucewa hakan sai ya zama matsala, to shine yasa aka yi kofofi.”

Ya kuma ce kowacce kofa akwai Maigadinta wanda ake cewa Sarkin Kofa.

“Kamar Kwamanda ne na sojoji, kuma akwai sojoji a karkashinsa, shiyasa duk wata kofa zaka ga akwai gidaje na Sarkin Kofa da kuma Dakarunsa, koda wata matsala za ta taso, ko idan za’a kawowa Kano farmaki, to kafin a kawo sojoji daga cikin gari, to su sojojin da yake tare da su za su yi maganin abin,” in ji Dr. Tijjani.

Muhammad Sunusi Al-Mustapha, Sarkin Kofar Dawanau na goma sha biyu (12), ya bayyana ayyukan Sarkin Kofar Dawanau tare da bayyana tarihin Kofar ta Dawanau.

“An yi ta ne saboda tsaro, kuma Sarkin Kofar Dawanau yana da dakinsa saboda tsare abokan gaba idan za su shigo, shi wannan kyaure akwai karamar kofa a jikinsa, idan mutane suka zo sai an leka an gano idan ba abokanan gaba bane sai a bude,” in ji Sarkin Kofa.

Dr. Naniya ya ce sannu a hankali tarihin wadannan kofofi na gushewa, musamman ganin yadda wasu abubuwan kofofin ke bacewa.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zumunta, domin samun labarai da dumi-duminsu.

Facebook: https://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitter: https://twitter.com/jaridarhausa

Email: info@jaridarhausa.com

This Post Has 2 Comments

  1. ibrahim tukur

    Allah ya Kara Daukaka Muna jin dadin yanda kuke fadar gaskiya kome dacenta

    1. Jaridar Hausa

      Mun gode Malam Ibrahim kwarai da gaske

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.