Wani mutumi ya shekara 16 yana kwanciya gado daya da gawar matarshi

Wani mutumi ya shekara 16 yana kwanciya gado daya da gawar matarshi

Mutane da yawa suna matukar shiga damuwa idan suka rasa masoyi, wani mutumi dan kasar Vietnam, ya tono gawar matarshi ya sanya ta a cikin gunki yake kwanciya da ita a gado daya na tsawon shekaru 16.

A lokacin da labarin Mr Le Van ya bazu a shekarar 2009, mutane da yawa sun dauka kage ake yi masa, da yawa sunki yadda da cewa mutum zai iya zuwa ya tono gawar matarshi daga makabarta, ya kawo ta gida ya kuma dinga kwanciya da ita a gado daya.

Sai dai wannan shine abinda Mr Le Van ya dinga yi na tsawon shekaru 16, duk kuwa da irin sukar da yake samu daga wajen ‘yan uwanshi da abokan arziki na kauyensu, mutumin bai da niyyar mayar da ita kabari.

Mr Van da matarshi sunyi aure a shekarar 1975. Lokacin basu ma san junansu ba ballantana ayi zancen soyayya, iyayensu ne kawai suka hada su aure tun suna yara. Bayan auren sai soyayya ta shiga tsakaninsu, suke zamansu cikin jin dadi da soyayya.

Sun haifi yara bakwai, sai dai wata rana a shekarar 2003, lokacin Mr Van yana wurin aiki kawai sai labari yaji cewa matarshi ta rasu. Cikin gaggawa ya nufi gida, yana zuwa yaga fuskar matar nashi na dan lokaci sai aka binne ta.

Da farko, Mr Van ya koma rayuwa a cikin makabarta ne kusa da kabarin matarshi, inda yake kwana a wajen. Amma daga baya sai sauyin yanayi ya fara damunshi, irinsu sanyi da zafi. Sai ya yanke shawarar tono gawar matar tashi domin ya kaita gida ya cigaba da kwanciya da ita. Ba a jima ba ‘ya’yanshi suka gano cewa yana kwana a makabarta, kuma suka hana shi kwana a ciki. Duk da haka ya kasa daina tunanin matar tashi.

Cikin wani dare Mr Le Van yaga cewa tunda an hana shi kwanciya a makabartar bari ya kawo ta gida kawai. Da farko ya hako kasusuwanta ya sanya su a cikin wata jaka, sai kuma ya fara hada wani gunki mai siffar mace, ya sanya kasusuwan a ciki. Ya kawo ta gida ya kwantar akan gado kullum yake kwanciya kusa da ita. Ya kwashe shekaru 16 yana kwanciya da ita a gado daya.

Bayan ‘ya’yanshi sun gano abinda yayi, sai suka fusata suka bukaci ya mayar da gawar mahaifiyarsu cikin kabarinta, amma yaki, yace musu ba zai iya rayuwa ba idan babu ita. Makwabta sun daina zuwa gidanshi bayan sun gano cewa ya kawo kasusuwan matarshi cikin gidanshi yana kwana da ita. Wasu ma har sun sanar da jami’an tsaro cewa Le Van zai kawo cuta garin. ‘Yan sanda sunyi kokarin rarrashin shi akan ya mayar da ita, amma mutumin nan yaki yadda, sai suka hakura.

Mr Le Van kullum shine yake goge ta ya yi mata kwalliya ya canja mata kaya, abinda baya yi a lokacin da matar tashi keda rai.

“Lokacin da matata ke da rai, bata sanya kaya masu kyau sosai, yanzu dole na nema mata kaya masu kyau. Ina canja mata kaya sau biyu kullum,” Le Van ya ce. “Mutane na cewa na haukace saboda ina kula da gawa, amma ni na san cewa koda yaushe tana tare dani. Zan cigaba da kwanciya da gawarta har lokacin da zan bar duniya.”

Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

Facebookhttps://www.facebook.com/jaridarhausa

Twitterhttps://twitter.com/jaridarhausa

Emailinfo@jaridarhausa.com

Rubuta Sharhi Idan Kuna Da Shi.